Labaran Wasanni Tare Da Bala Branco

A yanzu hankali ya karkata ne ta wajan shirye shirye domin fafata wasannin neman shiga gurbin cin kofin duniya na shekarar 2018 wanda za'ayi a kasar Rasha

Za'a ci gaba da wasannin ne gobe Alhamis 6/10/2016 wasan da zai dauki hankalin ma'abuta son wasan kwallon kafa a duniya shine wasan da za'a kara tsakanin Itali da Spain a can kasar Italin

A Nigeria kuwa itama tana ta shirye shirye domin fafata wasan neman shiga gurbin cin kofin duniya na shekarar 2018, inda a yanzu haka filin sansanin horas da ‘yan wasan Super Eagles dake Abuja ta cika da manya manyan ‘yan wasan kwallon kafa na Nigeria da suke kasashen waje.

Cikin ‘yan wasan da suka samu isowa a kwai kaftin Mikel Obi na Chelsea da Ahmed Musa dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, sai Kelechi Iheanacho na Man City da kuma sauran manyan ‘yan wasa na waje da na gida har su 23 da aka gayyata.

Nigeria dai zata kara da takwarar ta Chipolopolo ta zambiya ne ranar lahadi 9/10/2016 a can kasar zambiya.

Kafin wannan ranar Super Eagles zata gwabza da kungiyar Plateau United ta garin Jos domin gwajin karfin ‘yan wasanta a Abuja.

Mai horas da ‘yan wasan na Super Eagles Gernot Rohr yace yana da karfin gwiwar cewa yaransa zasu samu nasara akan zambiya.

Your browser doesn’t support HTML5

Labaran Wasanni Tare Da Bala Branco