Bincike ya nuna kungiyar kwallon kafa ta Man Utd ke kan gaba wajan jerin sunayen kulob din da suka fi amfani da ‘yan wasa mafi tsada a kakar wasan bana a yankin turai na shekara 2016.
Manchester tana amfani da ‘yan wasan da addadin kudinsu ya kai fam miliyan £627.7.
Sai Real Madrid a mataki na biyu fam miliyan £554.2
Man City na matsayi ta uku da fam miliyan £533.9
Kungiyar kwallon kafa ta Swansea city ta baiyana sanarwar korar mai horas da Kungiyar mai suna Francesco Guudolin, daga mukaminsa a ranar da yake murnar cika shekaru 61 da haihuwarsa.
Kungiyar ta maye gurbinsa da Bradley tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Stabaek ta kasar Norway wada zai fara wasansa da Arsenal ranar 15/10/2016.
Kungiyar ta Swansea ta ce ta dakatar da Francesco saboda rashin tabuka wani abin kirki a wasanni 7 da yayi na premier league inda yake da maki 4 a matsayi na goma sha bakwai.
Itama Aston Villa ta bi sahon kuren mai horas da ‘yan wasan kungiyar, ta kori Roberts Di Matteo da Kungiyar. Ita dai Aston Villa tana mataki na 19 ne a gasar Championship a kasar Ingila.