Tashoshin Jiragen Sama Da Su Kafi Haddura A Fadin Duniya!

Tashashoshin

Tashoshin jirgin sama “Airport” wurine da milliyoyin mutane kan hadu a fadin duniya, wadansu kuwa suna iya zama matattarar da wasu basu sha’awar zuwa. Wani rahoto da aka fitar da yayi nuni da tashoshin jirgin sama da su kafi hadari a fadin duniya.

A rahoton dai anyi amfani da yadda yanayin tashoshin suke wajen tantancewa, domin kuwa wasu idan mutun ya sauka har bayaso ace lokacin tashin shi yayi, amma wansu kuwa dan bakara. Haka wajen mu’amala tsakanin ma’aikata da fasinjoji yana iya zama da kyau haka yana iya bata rayuwar mutane da dama.

Tashar jirgin Paro, Bhutan, itace wadda tafi kowannen hadari a duniya, domin kuwa idan akayi maganar duk wasu abubuwan jin dadin rayuwa da ya kamata a samu a filin jirgi babu su, sai na biyu shine Toncontin, Tegucigalpa, Honduras, kana Manila Ninoy Aquino International Airport, na kasar Philippines.

Filin jirgin saman Heathrow, dake kasar Ingila, na daya daga cikin tashoshi da jirage su kafi sauka a duniya, sai filin jirgin sama na kasa-da-kasa na Sarki Abdulaziz, dake kasar Saudiyya. Na gaba kuwa shine filin jirgin Taipei Taoyuan, na kasar Taiwan.

Kana Tribhuvan, a kasar Nepal, haka filin jiragen Shanghai Hongqiao dake Shanghai, China, yana daga cikin jeri. Filin jirgin sama na LaGuardia Airport, jihar New York, da Los Angeles a jihar California, sun shiga sahun tashoshi da su kafi hadari a fadin duniya.