Wasu kadan daga cikin alamomin da masoya, zasu iya gane cewar ko dai budurwa na son saurayi ko shima yana sonta. A duk lokacin da daya ya aika ma wani rokon zama abokai musamman a shafin yanar gizo, kamar facebook, Instagram, text, da dai makamantan su, amma ba’a amsa mishi ba. Haka idan mutun yaga budurwa ko saurayi, basa maganar juna a shafufukan yanar gizo, to akwai lauje cikin nadi.
Kana idan saurayi nama budurwa maganar yadda rayuwar su zata zama a gaba, idan sunyi aure, da suka shafi ‘ya’ya nawa zasu haifa, da irin dai yadda ya kamata su gudanar da rayuwar su, to shima alamu ne da mace ke nuna ma saurayi ba’a tare.
Idan budurwa bata magana da saurayin ta, akan abubuwa da suka shafi rayuwar ta, ko wasu abubuwa da suka shafi gidan su, dai zai nuna ma saurayi ta damu da shi, tunda har tana shawara da shi. Idan hakan baya faruwa, to akwai bukatar binciken tarayyar su.
Idan mace bata gabatar da saurayi a wajen kawayen ta, da danginta ba shima wata alamace, da take bayyanar da rashin damuwa da mutun, ko saurayi ya bukaci budurwa ta gabatar da shi ga iyayen ta, sai tace ba yanzu ba, to akwai abun dubawa.
Wani abu mai muhimanci, idan budurwa bata damuwa da abun da zai bata maka rai, ko bata damuwa da wasu abubuwa da suka faru da kai a baya, to yana da kyau mutun ya kara bincikar zaman takewar su.