'Yan Sanda Sun Kama Wani Shehun Malami

Tayyib Erdowan

‘Yan Sandar Turkiya sun kama wani dan uwan shehun malamin nan dan kasar Turkiyya dake zaune a nan Amurka mai suna Fetuhullah Gulen, wanda ake tuhumarsa da yunkurin juyin mulkin da aka nemi yi a watan Yuli don kifar da gwamnatin shugaba Racep Tayyib Erdowan da bai yi nasara ba.

An tsare Kutbettin Gulen a lardin Izmir na yammacin Turkiya bisa zargin alakarsa da kungiyar ta’addanci kuma yan sanda na masa tambayoyi, inji ma’aikatar dillancin labarai ta kasar ta Anadolu.

Kutbettin shine dan uwan Gulen na farko da aka fara tsarewa tun bayan yunkurin kifara da gwamnatin kasar.

A cikin watan Yuli hukumomin kasar Turkiyyar suka cafke wani dan’uwan Gulen din, shi kuma ana kiransa Gulen Muhammed Sait Gulen a birnin Erzurum dake gabashin kasar.

An kuma kara kama wani dan uwansa mai suna Ahmet Ramiz Gulen a cikin watan Agusta a birnin Gaziantep dake kudu masu gabashin kasar .

Shi dai wannan shaihin malamin na Turkiyya Gulen, wanda tun shekarar 1999 yake zaune a nan Amurka, wanda kuma acan da tsohon na hannun daman shugaba Erdogan ne, hukumomin Tukriyya ne suke zarginsa da kitsa makircin wannan juyin mulkin da aka so yi ran 15 ga watan Yulin wannan shekarar da muke ciki, amma ya sha musanta zargin.