Wannan sanarwar gargadin, ta yi nuni da cewa akwai yuwuwar barkewar rikici a wasu yankunan Kinshasa da sauran manyan biranen kasar.
Rikici dai ya barke a kasar ta Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ne, saboda aniyar shugaba Jospeh Kabila ta ci gaba da zama a kan karagar mulki.
Daga ranar 19 ga watan Disamba ne wa’adin Kabila zai kawo karshe, wanda hakan ke nufin zai kammala wa’adinsa na biyu ke nan kamar yadda doka ta tanada masa, domin kundin tsarin mulkin kasar bai amince da yin wa’adin na uku ba.
Sai dai hukumar zaben kasar ta ce ba za ta iya gudanar da zabe ba har sai a karshen shekarar 2018.
Shi dai Shugaba Kabila bai ce komai dangane da haka ba, amma masu lura da al’amura sun ce yana yunkuri ne ya ci gaba da zama akan karagar mulki, lamarin da ke haifar da mummunar zanga zanga a kasar,wacce ke tsakiyar Afrika.