WASHINGTON D.C —
Bisa al’ada lokacin bukukuwan babbar sallah lokaci ne da mata ke yin hidindimu na sarrafa naman layya da aka yanka mussaman ma ga wadanda suka samu damar yin Ibadar layya.
Wata uwa, Hajiya Zulai Mustapha ta ce bayan mai gida yayi yanka an kuma bada na sadaka da kyauta ga makwabta da ‘yan uwa, ragowar naman takan soya, ko ta yi dambu da shi, sannan ta gyara tare da ajiye wani a firjin domin yin amfani da shi daga lokaci zuwa lokaci.
Ta ce wani lokacin idan an soya naman akan raba ga wadanda ba’a ba su danye ba, domin murnan zagayowar babbar sallah.
Hajiya Zulai ta ce ana zuba kayan kamshi don nama yayi gardi ga masu ci.
Dopmin Karin bayani saurari cikakkiyar hirar a nan.
Your browser doesn’t support HTML5