Aikata Wani Abu A Wata Kasa Laifi Ne, Awata Kasar Lada Ake Bayarwa!

Kifin Salmon

Kusan kowace kasa a fadin duniya, nada tsare-tsare da dokoki, da a wasu kasashe ba abun damuwa bane. Abincin wani gubar wani. A kasar Birtaniya, a shekarar 1986, an gabatar da wata doka, da ta hana kama kifi mai suna “Salmon” wanda idan aka samu mutun, da laifin kama irin wannan kifin, za’a yanka mishi tarar da zata kai $6,500 dai-dai da naira milliyan biyu da dubu dari biyar, ko zuwa gidan kasu.

A kasar China, cikin shekarar 2013, an saka dokar duk yaro balagagge da bai ziyarci iyayen shi ba, akai-akai ba, shima za’a hukun tashi. Kowanne yaro dole ne ya ziyar ci iyayen shi duk bayan kwana biyu, da kuma kokarin taimaka musu, rashin yin hakan zai sa a yanka ma, mutun tara ko gidan kasu.

A kasar Ingila kuma idan hukumomin gwamnati, suka aika ma mutun da wasika, bayan wasu kwanaki idan mutun bai rubuta amsa ba, shima za’a iya yanka mishi tara, da takai $1,300 idan kuma mutun ya karyata amsar wasikar, kudin zasu iya komawa $6,500 dai-dai naira milliyan biyu da dubu dari biyar, ko gidan kasu na wasu shekaru.