Shugaban ya bayyana cewa dalilin da yasa tunda farko jam’iyyar ta kuduri aniyar cewar zata yi zama da ‘yan majalisar dokokin jiha, da na tarayya, da kuma mai girma gwamna daga bisani kuma sai ta yi zaman gabaki daya, wanda duk bayan watanni uku za’a rika ganawa domin sanin inda bukatar gyara ko kuma yin sassauci ga wasu lamurran.
Ya kara da cewa kamata yayi duk dan jam’iyyar APC mai kishin jam’iyyar ya jawo hankalin sauran ‘ya’yan jam’iyya a duk lokacin da ya hangi wani abu da bai dace ba a maimakon akai kasuwa a baje koli.
Sai dai kuma a dai dai lokacin da shugaban yake ganawa da shuwagabannin uwar jam’iyya domin neman maslaha kan rikicin jihar, matasan jihar sun yi dafifi a harabar ofishin jam’iyyar inda suke nuna rashin goyon bayan gwamnan jihar.
Galadima Abba Itas ne ya jagoranci matasan kuma ya bayyanawa wakiliyar sashen Hausa Madina Dauda cewar taron ya sami asali ne sakamakon irin halin da jama’a suka sami kawunansu domin kuwa a cewar sa, Allha ya hada su da shugaba maras tausayi, shi yasa jam’iyya ta taso cikin gaggawa domin shiga tsakani tun kafin matsalar ta yi nisa, domin a cewarsa idan tafiya tayi tafiya kuma aka ci gaba da samun matsala irin wannan, babu shakka jam’iyyar zata sami matsala.
Jagoran matasan ya kara da cewa acikin matsalolin da ake fuskanta a jihar sun hada da rashin biyan albashin ma’aikata har na tsawon watanni biyar zuwa shidda, ba’a biya ‘yan fansho ba, kuma ga korar ma’aikata.
Shi kuwa mai ba gwamna shawara a harkar manema labarai Sabo Muhammed ya yi tsokacin cewar gaskiyar lamarin itace idan wannan wata yak are ne ma’aikatan ke bin gwamnatin jihar albashin watanni biyu, sai kuma kananan hukumomi saboda ana kan tantance su a yanzu haka.
Domin Karin bayani ga rahoton Madina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5