Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry Ya Jinjina Ma Kungiyoyin Sa Kai A Najeriya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya jinjina ma kungiyoyin sa kai da ke aiki a Najeriya, saboda himmar da su ke badawa wajen habbaka al'ummomi, da yaki da rashawa da cin hanci da sauran matakan gina kasa.

Kerry ya gana da wakilan kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa da kuma wata tawagar 'yan mata da ke cikin shirin nan na musamman na Kimiyya da Fasaha da Injiniya da kuma lissafi, wanda ake kira STEM a takaice, a Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja, babban birnin Naijeriya jiya Laraba.

Kungiyoyin rajin yaki da cin hanci a Najeriya dai sun bukaci Kerry da ya taimaka a hanzarta maido da biliyoyin dalolin da jami'an gwamnatin kasar su ka wawure.

Sun yi imanin cewa kudin da aka sacen na bakunan kasashen yamma ko kuma wasu kadarorin bankunan a kasashe irinsu Amurka da Burtaniya da Switzerland da kuma wasu kasashen Turai.

Kerry ya gaya ma kungiyoyin cewa batun kwato kadarori al'amari ne mai wani tsarin da ke da matukar wahala to amma gwamnatin Amurka na da wasu lauyoyi da akantoci da ke aiki akai.