Kasar Brazil Ta Yi Bankwana Da Wasannin Olympic Da Ta Dauki Bakunci

Kassar Brazil wadda ta dauki bakuncin gasar Olympic dama sauran kasashen duniya da suka halarci gasar ta tsawon kwanaki 16 suna ban kwana da wannan taron.

Taron wanda ya kunshi abubuwan birgewa da ban haushi wata sa'a wadannan abubuwan suna dushe ainihin ita gasar kanta.

Dubun dubatar 'yan kallo sun jurewa yawan ruwan sama da iska da kura domin kawai su kashe kwarkwatar ido ta rufe gasar wadda aka yi a filin wasan Maracana.

Bikin wanda shine cikamakin gasar kuma ya hada da liyafar cin abinci wadda daga wannan sai kuma wadda ake fata ayi a cikin shekarar 2020 a kasar Japan.

Wasan karshe na gasar shine wanda aka ci gwal 12 ciki ko harda gasar kwalon Kwando ta maza.

Kasar Amurka ce ta yi fafatawar karshe da kasar Serbia kuma aka tashi ci 96 da 66, inda Amurka ta lashe kuma wannan shine karo na ukku da Amurka ke lashe gasar a jere.

Ga wadanda suka dauki na biyu ko an fafata ne tsakanin Spain da Australia, inda Spain ta samu jefa kwallaye 89 a ragar Australiya wadda ita kuma ta jefa 88.