Kimanin fursinoni tamani ne da aka yankewa hukumuci daban daban ke fama da tabin hankali, a gidan yari dake jihar Abia.
Kakakin hukumar gidajen yarin jihar ta Abia, DSP, Kalu Ikpe, ne ya bayyana wa manema labarai, a Umuahia, yana mai cewa a wasu lokuta a kan sami wasu kasu fama da ciwon kwakwalwa ko a Umuahia, sa a kwashe su zuwa garin Aba, inda ake da wajen kula dasu.
Ya kara da cewa hukumar na lura da masu tabin hakalin ta yadda ake sa ran cewa zasu iya fuskatar kuliya domin a yi masu shara’a a kan laifuffukan da ake tuhumar su da shi.
Kakakin ya ce idan har rashin lafiyar ya ci gaba da tabarbarewa har ta kai ga yafi karfin su sai su sanar da kotun da ta basu ajiya domin acewarsa kotu da kuma Alkalin Akalan jihar ne ke da hurumin salamar marasa lafiya,