Jami'an Hukumar Tsaron Farin Kaya 92, Sun Sami Horo Na Musamman A Maiduguri

Jami’an hukumar tsaron farin kaya da aka sani da suna Nierian Security and Civil Defence Corps guda 92, sun kammala horo na musamman akan dabarun amfani da makamai domin tabbatar da inganta ayyukan tsaro da kara tabbatar da nasarar da jami’an soji suka samu ta murkushe ‘yan ta’addan boko haram a arewa maso gabashin Najeriya.

An gudanar da bukin kammala horaswar ne a dandalin Youth of Maimalari Contonment wanda rundunar sojin Najeriya ta 7, ta shirya, kuma an bayyana irin dabaru daban daban da jami’an suka sami horo a kai wadanda suka hada da dabarun iya kare kai.

Da yake Magana a lokacin da ake gudanar da taron, shugaban horaswar laftanar kanar Nnaji ya bayyana cewa jami’an sun nuna hazaka da kuma kwarewa wajan amfani da makamai.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa babban jami’in ya bayyana cewa daliban sun nuna kwazo kwarai wajan motsa jiki da kuma mayar da hankali wajan daukar darussan da aka koya masu.