RIO 2016: 'Yar-Wasan Tsallen Amurka Zata Kafa Tarihi A Duniya!

'Yar wasan tsalle Simone Biles

Shahararriyar ‘yar wasan tsalle Simone Biles, ‘yar kasar Amurka, tana kokarin kafa tarihi a duniya. A yunkurin ta na neman lashe tagulla biyar a wasan Olympcs, a tarihin duniya. Yanzu haka dai ta samu nasarar lashe guda uku, tana shirin fuskantar wasannin biyu da suka rage mata.

A jiya Lahadi, dai ‘yar tsallen ta samu ‘yar tangarda kadan, inda yanzu take da maki goma sha biyar da digo tara, ta doke abokiyar hamayyar ta Maria Paseka ‘yar kasar Rasha, inda take da maki goma sha biyar da digo biyu. Ita kuwa Giulia ta kasar Switzerland, ta tafi gida kyautar azurfa.

Zuwa yau dai, makin Biles shine makin da yafi na kowa, wanda tayi wani shahararren tsalle, da ya samar mata wannan makin mai yawa. Matashiyar mai shekaru goma sha tara ‘yar jihar Texas ce a nan kasar Amurka. Ana sa ran idan har ta lashe wasannin biyu masu zuwa, zata bar tarihi a fadin duniya, inda ba’a taba samun wanda yayi abun da tayi ba.