Kwastam Sun Kama Manyan Tireloli Dauke Da Kajin Gwangwani Da Aka Sarrafa Da Sinadarin Aje Gawa

Hukumar kwastam ta zone C dake Owerri, a cikin ayyukanta na hana shigowa da haramtattun kayayyaki ta barauniyar hanya a Najeriya, ta tabbatar da kama katan dubu ashirin da hudu da dari biyu da saba’in da bakwai N24,273, na kajin gwangwani da kudin harajinsu suka kai kudi kwatankwacin Naira miliyan dari biyu da hamsin da shidda da dubu dari biyu da sittin da hudu da dari biyu, N256,264,200.

A jawabinsa na ranar litini, jami’in hulda da jama’a na bangaren ya bayyana kalaman babban kwantirolan hukumar jihar Haruna Mamudu cewar an kama kayanne wadanda aka kumshe cikin hikima a wata mota da aka rubuta sunan kamfanin “DHL” a yankin Benin dake jihar Edo.

Jami’in ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a dakin da hukumar ke tara kayan data kama ya ce kudin dutin kayan kawai sun kai yawan adadin kudin da ya bayyana bayan jami’an dake sintiri da akaiwa lakabi da eagle eye sun cafke mutane uku da ake zargi.

Mamadu kamar yadda mujallar daily post ta wallafa ya kara da cewa yayi matukar kaduwa ganin yadda ake amfani da sinadarin da ake amfani dashi wajan adana gawa wajan sarrafa kajin da ake shigowa dasu daga kasashen waje ta barauniyar hanya wanda hakan yana haifar da rasa rayuka da dama a fadin kasar a sakamakon hakan.

Daga karshe ya bayyana cewa hukumar zata ci gaba da yin iyakacin kokarinta domin tabbatar da dakile fasa kwauri da shigo da haramtattun kayayyaki da kuma fadakar da jama’a akan hadurran dake tattare da amfani da irin wadannan kaya.