Ko Mijinta Ya Amince Bazata Yi Ba

Fatima Abubakar

A shirinmu na nishadi a yau mun sami Bukuncin sabuwar jaruma a harkar fim industry wato Fatima Abubakar wacce aka fi sani da sai na aure Zango ko Fati Shu’uma .

Ta ce ta fara harkar fim ne sanadiyar wani dan fim da ya zo wani shagon “yar uwarta domin daukar fim, daga nan sai ta fara sha’awar kasancewa ita tana fitowa.

A cewar jaruman daga inda aka fara kennan ko da yake da farko Iyayenta basu amince ba sakamakon irin kallon da ake yiwa ‘yan fim daga nesa.

Amma daga bisa suka fahimci cewar sana’a ce mai kyau suka kuma amince ta fara fim, ta ce burinta bai wuce tayi aure ba da zarar tayi aure ko da kuwa maigidanta ya amince mata tayi fim bazata yi, a muradin ta da zarar tayi aure sana’ar fim ya kawo karshe.

Your browser doesn’t support HTML5

Ko Mijinta Ya Amince Bazata Yi Ba - 3'41"