An Taba Kwantar Da Matashin Da Ya Hallaka Mutane 9 A Birnin Munich A Asibitin Tababbu

Masu bincike a kasar Jamus sunce matashin nan da ya kashe mutane Tara ranar Juma’a a birnin Munich na jihar Bavaria, ya samu kulawa a asibitin tababbu, kuma ya kwashe sama da shekara guda yana shirya kai harin.

Cikin shekara ta 2015 an kwantar da matashin mai shekaru 18 da haihuwa David Ali Sonboly a asibiti, har na tsawon wata biyu, kafin a sallame shi tare da ci gaba da bashi kulawa, a cewar mai magana da yawun jami’an tsaron Munich Thomas Steinkrau-Koch.

Mr Steinkraus-Koch, yace bayan halin da matashin ke ciki na damuwa, ana kyautata tsammanin ya na fama da tsoron cudanya da jama’a.

Sonboly, wanda ya kashe kansa bayan da ya kai harin, haka kuma ba wai ya zabi wasu nau’in mutane ba ne lokacin da ya kai harin, kuma babu wata shaida da ke nuni da cewa harin na da alaka da siyasa.

Manyan jami’an tsaron birnin Munich sunce kamata yayi sojojin Jamus su kai ‘dauki a duk alokacin da shiga irin wannan hali kamar irin wannan na ranar Juma’a da ya faru.