Dan wasan gaba na kungiyar Super Eagles Kelechi, Iheanacho, wanda yanzu yake takawa kungiyar Manchester City, na Ingila wasa ya sami shiga cikin ‘yan wasa goma da suka fi taka leda a duniya a ‘yan kasa da shekaru ashirin da daya.
An sami wani sakamako ne a bincike da majallar Soccerex ta gudanar akan ‘yan kwallon da aka haifa bayan 1, ga watan yuli na shekarar 1995.
Kelechi wanda ke takawa Manchester City, ta maula shine na tara, a duniya a wannan rukunin ‘yan wasa sauran sun hada da Anthony Martial,na Manchester United, Leroy Sane mai takawa Schalke, wasa da Renato Sanches, na Bayern Munich.
Har da sunayen Breel Embolo, na Schalke da Marcus Rashford mai murza leda a Manchester United, Max Meyer Schalke da Julian Weigl na kungiyar Borussia Dortmund ta kasar Jamus.