Sunayen masu horas da yanwasan kungiyar Super Eagles ta Nigeria wandanda hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Nigeria ta fitar a daren jiya 18/7/2016 sakamakon zama da komiti tayi sune:
Paul Le Guen (Technical adviser)
Salisu Yusuf (Chief Coach)
Imama Amapakaho (Assistant)
Aloy Agu (Goal keeper Trainer)
Bitrus Bewarang (National Tech Director)
Sai kuma Nduka Ugbade (Assistant coach U -17)
A bangaren hada hada yanwasan kwallon kafa kuwa, sabon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Man City Pep Guardiola na neman danwasan Arsenal maisuna Hector Bellerin
Kingiyar kwallon kafa ta Juventus dake kasar Italy ta baiyana zunzurutun kudi har fan miliyan 50 ga kungiyar Man City in har tana son danwasan ta maisuna Leonardo Bonurci dan shekaru 29 da haihuwa.
Ita kuwa kungiyar Napoli na neman kudine har yuro miliyan €94.7 daga kungiyar Juventus in har tana bukatar dan wasanta Gonzalo Higuian kafin ta sayar mata dashi.
Yayin da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ke kokarin sayen masu tsaron baya har su biyu
Jason Denayer danshekaru 21, daga Man City, sai Matthias Ginter danshekara 22, daga Borussia Dortmund
Kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da Barcelona da Manchester United da kuma chelsea na zawarcin danwasan Valencia Andre Gomes dan shekara 22 akan zunzurutun kudi fan miliyan £54.