Paul Pogba Ya Kasance Dan’wasan Da Yafi Tsada A Duniya

A yanzu haka danwasan Kungiyar juventus mai suwa Paul Pogba ya kasance dan’wasan da yafi kowane dan wasa tsada a duniyar kwallon kafa bayan da kungiyar kwallon kafa ta Man Utd ta amince da sayen Paul Pogba akan zunzurutun kudi har yuro miliyan €110 na tsawon shekaru 5.

Pogba zaike karbi kudi har yuro miliyan €13, a kuwaCE karshen shekara, Pogba wanda ya bar kungiyar Man Utd a shekara ta 2012, ya koma Kungiyar Juventus ta kasar Italy kyauta wato ( free transfer ) alokacin da Sir Alex Ferguson yake rike da kungiyar.

Sai dai kuma masu fashin baki akan wasannin kwallon kafa suna ganin darajar Pogba bata kai wannan kudin ba, ana sa ran zai rattaba hanu da Man Utd nan da wani lokaci kadan.