Dare Daya Allah Kanyi Bature! Bayan kwashe watanni shida 6, ana cigiyar gwarzon da ya lashe zunzurutun kudade masu yawa, na gasar cacar kudin mairabo. A kasar Amurka akan gudanar da cacar mai rabo, a duk shekara wanda mutane sama da milliyan dari ke shiga cikin gasar.
Abu kawai da ake bukata mutun yayi shine, ya siya katin cacar koda kuwa na dalla daya ne $1, wannan zai sa mutun cikin jerin masu bukatar samun nasara. A wannan shekarar an bayyanar da wanda ya samu nasarar lashe zunzurutun kudi da suka kai dallar Amurka billiyan daya da milliyan shida $1.6B dai-dai da naira billiyan dari hudu da tamanin N480,000,000,000. Ita dai wannan cacar da ake kira “Powerball jackpot” ta mai rabo ce, wanda a bana Mr. Marvin da matar shi Mae Acosta, daga jihar California, su suka samu rabon.
Sun bayyar da wannan a matsayin babbar nasara da ba zasu taba mantawa a tarhin rayur suba. Domin kuwa sun zauna cikin wani mawuyacin hali a rayuwa, sai gashi sun zamo biloniyoyi rana tsaka. Sun kwashe tsawo watanni shida don shiryama karbar wadannan kudaden ne, shi yasa basu bayyanar da kansu da wuri ba.