Hanyoyin Zama Haziki, Hafizi, Jarimi, Ma'abuci Dukiya!

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, Mai kudin duniya Bill Gate, Mai kudin Afrika Aliko Dangote.

Sakamakon wani bincike da aka gudanar, ya bayyanar da cewar a irin yanayin da mutun ya kwanta bacci, shike tabbatar da irin yanayin da mutun zai tashi da safe, da irin kuzarin da mutun zai tashi da shi.

Hakanan kuma an iya gano wasu abubuwa da idan mutun yanayin su a duk dare kamin bacci, zai dinga samun nasara a duk abun da yasa a gaba a rayuwar shi. Mutane da suke samun nasara a duk wani abu da su keyi a rayuwa, nada yakinin cewar nasarar su na zuwa ne a sanadiyar wadatacciyar lafiya da suke da.

Lafiya itace uwar jiki, wanda idan mutun baya sama kanshi tunanin da bashi da amfani, da kokarin samun wadataccen bacci, duk suna taimakawa wajen nasara a rayuwa. Idan mutun yana bukatar samun dacewa a rayuwa, to kada mutun ya kwnata bacci batare da yayi karatu ba, koda kuwa na jarida ne da wasu karatu da zasu karama kwakwalwar shi kuzari.

Hakan ya tabbata akan shugaban kasar Amurka, Barack Obama, da shahararren mai kudin duniyar nan Bill Gate, sun tabbatar da cewar a duk nasarar da suka samu a rayuwa nada alaka da yanayin karatun su, a duk dare kamin suyi bacci, su kan karanta littafi na kamar mintoci talatin 30. A cewar Michael Kerr, shahararren marubucin kasa-da-kasa, yasan ‘yan kasuwan duniya da suke da wannan dabi’ar ta karatu duk dare kamin bacci. Basu tsayar da kansu a karatun abu daya ba, sukan karanta duk wani abu da ya shafi rayuwar dan’adam.