Makomar Shafin Facebook Nan Da Shekaru Kadan Masu Zuwa!

Russia Putin

Kimanin shekaru goma sha biyar 15, da suka wuce, masana sunyi wani hasashe da suke ganin kamar cewar wasu shekaru kadan masu zuwa, duniya zata zama kauye daya. Wanda al’umma zasu dinga ganin kowa da magana cikin sauki, yanzu kuwa ana iya cewa hakan yazo.

Domin kuwa mutane kan iya magana da duk wanda suke so a fadin duniya. Wani babban abu da yanar gizo ta kara samarwa cikin sauki shine, yadda mutane suke yawan rubuce-rubuce, wanda a da mutane kanji wahalar yin rubutu. Amma a yanzu sai ga mutane kan shiga shafufukan su don magana cikin rubutu.

Yanzu haka dai masana naganin cewar, nan da kimanin shekaru biyar haka, duniyar kuma zata sake canzawa. Mutane zasu daina rubutu a shafufukan suna zumunci, za’a daina rubutu. Mai kula da hada-hadar sadarwar kamfanin Facebook, a kasashen turai Mr. Nicola Mendelsohn, ya bayyana hakan, da cewar mutane zasu koma amfani da bidiyo wajen magana, don isar da sakon su a fadin duniya.

Mutane da dama zasu dinga amfani da wayoyin su, suna daukar hotunan bidiyo da kuma aika su cikin sauki da gaggawa. A duk lokacin da mutun yake da bukatar yin hakan, kawai zai kunna wayar shi ko duk wani abu da yake amfani da shi, za’a dinga ganin shi kai tsaye a duk fadin duniya.