Wayar Kamfanin Samsung Galaxy S7 Ta Fadi Jarabawa!

Wayar Samsung Galaxy S7 Active

Wayar kamfanin Samsung mai suna Galaxy S7 active, ta fadi jarabawar da akayi mata, wayar dai an santa da sunan cewar ruwa baya shiga cikin ta. An dai gwada saka wayar cikin ruwa da ta kwashe kimanin minti daya da dakika biyar 1.5M kodai da aka cirota bata aiki.

A cewar rahoton “Consumer report” an sake saka daya wayar don jarabawa, wanda itama bata kai labari ba. Kamfanin dai sun bayyanar da cewar, lallai babu shaka wadanan wayoyin da akayi gwaji dasu, kila jikin su da ya kamata ace sun rufe basu rufe ba, wanda hakan yasa ruwa ya shiga cikin su. Amma suna da tabbacin ingancin wayar.

An saida wayar a kasuwar wayoyi ta kasar Amurka, da ma wasu kasashe, wanda bata samu karbuwa ba, a kasuwar wayoyi ta kasar Ingila. Yanzu haka dai kamfanin, sun dau alwashin sake duba nagartar wayar tasu da fadada hanyoyin da zasu inganta ta, haka da sauran abubuwan da suke kerawa.