Ana Dab Da Kammala Gina Wurin Yawon Shakatawa Mai Suffar Jirgin Annabi Nuhu

Ana daf da kaddamar da kwatankwacin jirgin Annabi Nuhu, da suka yi amfani da shi da dadabbobin da suke ciki, suka tsira daga ruwan tufana, a zaman wurin yawon shakatawa, a jihar Kentucky dake tsakiyar Amurka, wannan karon ba tilas bane masu ziyara su kwai-kwayi daukar jinsunan halittu daban daban a jirgin ba.

Rahotanni sunce an gina jirgin kusan kamar na Annabi Nuhu, kamar yadda aka sami bayanai cikin linjila watau Bible. Jirgin yana da tsawon mita 155, girmansa ya kai tsayin bene bakwai, kan kudi dala milyan dari. Ana sa ran dubban mutane ne zasu kai ziyara wurin.

Shugaban wata majami'a data gina wurin yawon shakatawar Ken Ham, yace wurin zai kasance babban wurin ziyara na tarihin addinin kirista mafi girma irinsa a duniya.

Amma wata tawaga ta wadanda suke adawa da ko wane irin addini, watau wadanda basu yarda da Allah ba, sunce wurin yawon shakatawar bashi da wani makamancinsa saboda yayi watsi da ilimin kimiyya baki daya.

Akwai masu sukar lamirin shirin, wadanda suka zargi gwamnatoci daga ko wane mataki a jihar da suka baiwa gandun rangwamen haraji kimanin dala milyan 80 cikin shekaru 20.