Makoni biyu da suka shige Mallam Umar Mohammed ya kama wani da ake kyautata zaton dan kungiyar Boko Haram ne wanda yake kokarin shiga birnin Maiduguri arewa maso gabashin Najeriya, dauke da bam.
Mallam Umar yace ya kama mutumin yaje ya danka shi hannun kwamandan sojoji. Jami’an tsaro sai suka kwance bam din da mutumin yake dauke da shi.
Shi dai Mallam Umar Mohammed dan shekara tatalin da biyu da haihuwa yana cikin kungiyar yan aikin sa kai da gwamnatin jihar Borno ta amince da kafuwarta a shekara ta dubu biyu da goma sha uku domin ta taimaka wajen yaki da ‘yan Boko Haram.
Kungiyar Boko Haram tayi shekaru bakwai tana razanar da yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma tapkin Chadi. 'Yan kungiyar Boko Haram sun kashe fiye da mutane dubu ashirin suka kuma tilastawa kimamin mutane miliyan biyu da dubu dari bakwai arcewa daga gidajen su.
To amma Alhamadullilahi kokarin da sojoji suke yi ya kasara yan kungiyar ta Boko Haram da kuma fatattakar su daga yankunan da dama.
A halin da ake ciki kuma, daga can Sokoto birnin Shehu, wakilin sashen Hausa Mustala Faruk Sanyinna ya aiko mana da rahoton jawabin barka da sallah na mai alfarma, Sultan Sa’ad Abubakar.
Sarkin ya maida hankalin ne kan babbar matsalar rashin tsaro ba'a Najeriya, kade ba amma a duk fadin duniya, masamman kasashen Musulmai.
Yayi kira ga 'yan Najeriya, dasu tallafa tare da bada goyon baya ga kudirin gwamnatin Najeriya, na bunkasa sha'anin tattalin arziki da wadata kasa da abinci ta hanyar bada kullawar gaske ga sha'anin aikin gona.
Your browser doesn’t support HTML5