Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marayu Da Gajiyayyu Sun Sami Tallafi Daga Kungiyar Izala Reshen Jihar Oyo


ABUJA: Taron bada tallafi
ABUJA: Taron bada tallafi

A karo na hudu kungiyar Izala reshen jihar Oyo, ta rarraba kudade sama da Naira Miliyan 3 da turaman atamfa da yaduna ga marayu da zawarawa da gajiyayyu.

Kamar yadda shugaban kungiyar na jihar Oyo, Salisu Abdullahi, wanda yace a bana sun sami nasara a bangaren abin da ya shafi marayu da gajiyayyu da zawarawa, inda aka sami tallafin kudi na sama da Naira Miliyan uku, an kuma rawabawa sama da mutane Dubu ‘daya.

Wakilin Muryar Amurka Hassan Umaru Tambul, ya zanta da wasu daga cikin mutanen da suka amfana da wannan tallafi, Aminatu Bello, tace ta samu turmin atamfa da kuma wata takardar ambulan dauke da kudi cikinta, Amina dai ta nuna farin cikin ta ga taimakon da aka bata da kuma fatan Allah yasa Alkhairi.

Dayawa yara marayun da suka sami tallafin sun nuna jin dadinsu da kuma kasancewa cikin farin ciki da godiya.

Saurari cikakken rahotan Hassan Umaru Tambuwal daga Ibadan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG