Masana Binciken Sararin Samaniya Sun Tafi Don Shiga Duniyar Jupiter!

Shiga Duniyar Jupiter.

Yanzu haka dai masu binciken arzikin sararin samaniya na cigaba da tafiya cikin sararrin samaniya, a yunkurin su na zuwa duniyar watan “Jupiter” tun kimanin karfe hudu da mintoci gomasha takwas na daren jiya ne, masu binciken sararin samaniyar suka tashi don zuwa yawon binciken. Tafiyar dai zata dauke su kusan mintoci talatin da biyar kamin su ratsa zuwa cikin duniyar ta Jupiter.

Idan dai har basu iya cinma nasarar shigewa cikin duniyar ba a cikin mintuna kanana, wanda tafiyar ta kai kimanin kilomita billiyan biyu da milliyan takwas. Kuma zai dauke su dakika daya da dugo biyu 1.2, su dauki hoton duniyar, wanda idan jirgin nasu bai yi tafiya yadda ya kamata ba, ko aka samu wani karamin akasi.

To babu shakka aikin su zai koma baya, an kashe zunzurutun kudade da suka kai dallar Amurka billiyan daya da milliyan daya, don gudanar da wannan binciken. Zuwa wannan duniya na tattare da haddura masu yawan gaske, domin kuwa a tarihi ba’a taba zuwa duniyar ba, babu wanda yasan ya cikin duniyar yake. Hasalima babu wani mahaluki da ya taba kusantar duniyar balle yasan ya take, Idan dai suka samu nasarar shiga zasu kafa tarihi a duniya.