Tun bayan inganta shafin su da sukayi, kamfanin zumunta na Facebook, sun kara samun milliyoyin mutane a fadin duniya na amfani da shafin don samun bayanan abun da ke faruwa a fadin duniya. Shafin na facebook sun maida alamar kauna “like” na shafin su da yake dauke da tambarin F, zuwa tambarin hannu da yatsa sama.
Binciken da suka gudanar da ya bayyanar musu da cewar mutane da dama sun karbi wannan sabon canjin nasu matuka, fiye da yadda yake a da. Wannan canje canjen da kamfanin yayi a cikin ‘yan tsakanin nan, na kara nuna cewar kafar sadarwa ta facebook, nada karfi matuka wajen juya akalar yadda mutane suke gudanar da rayuwar su ta yau da kullun.
Binciken ya bayyanr da cewar kimanin sama da kashi 28% na mutane a kasar Ingila ne, kanyi amfani da shafin wajen samun labaransu a sati. Haka kashi sama da 41% na matasa dake zagayen kasa da shekaru talatin da biyar 35, ne su kafi cin gajiyar wannan shafin.