Yaki Da Sha Da Safarar Miyagun Kwayoyi Jamhuriyar Nijar Ta Cafke Matasa 58 A Iyakarta Da Najeriya

marijuana

Kamar yadda rahotanni daga jamhuriyar Nijar a makon daya gabata suka bayyana cewa kasancewar kasar a tsakanin ksashen dake kusa da arewacin Afirka yasa masu safarar miyagun kwayoyi ke neman hanyoyi na kutsawa cikin kasar domin sayar da su cikin kasar kokuma ketarawa zuwa kasashen magreb ko kuma kasashen larabawa domin yunkurin zuwa kasashen Turai.

A cewar babban alkali mai shigar da kara a babbar kotun binin Konni da sunan gwamnati Malam Musa Haruna, ya ce matasa ne ke shan kwayoyin, kuma sun sami nasarar cafke mutane hamsin da takwas 58, a wannan shekarar wadanda suka hada da mace guda akan iyakar kasar da Najeriya.

Rahotannin sun bayyana cewa acikin nau'in kwayoyin da matasasn ke sha sun hada da Tramol, da tabar wiwi, da sukudai da sauran su.

Shugaban kundumar birnin kwanni ya ce bazasu tsaya hakanan kara zube ba suna kallon matasa na lalacewa, domn a cewar sa duk idan kaga wanda kwaya ta haukata zaka ga cewa matashine, dan haka zasu kafa kwamitin da zai dauki alhakin bincike a kowane lungu da sako sako.

Ya kara da cewa anyi kira da wayar da kan jama’a akan illolin shaye shaye, da safarar miyagun kwayoyi domin matasa su bar wannan dabi’a, kuma a hana masu kawo kwayoyin da masu sayar da su. Matsalar shaye shaye tana hallaka matasa. Kamar wadanda suka sami matsalar tabin hankali a sakamakon shan kwayoyi idan aka yi masu magani sukan sami sauki, amma idan suka cigaba da sha, ko anyi masu maganin basa warkewa.

Ta dalilin haka ne a wannan shekarar aka kama masu sayar da kwayoyi da yawa da kuma masu zuwa wasu kasashe domin su kawo kwayoyi anan kasar, duk wannan kokarine da jami’an ‘yan sanda da jandarmomi suka yi.

Shugaban sufuri na birnin Konni cewa yayi jami’an tsaron na matukar taimaka masu a cikin tashohin da suke daukar fasinja inda yawancin matasan ke boyewa domin aikata wannan mugunyar dabi’a ta shaye shayen kwayoyi.

Yanzu haka dai ‘yan Nijar sun dukufa domin tabbatar da dakile wannan matsalar kamar yadda babban alkali mai shigar da kara da sunan gwamnati ya bayyana cewa zasu gurfanar da duk wanda suka samu da hannu.

Saurari cikakken rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Yaki Da Sha Da Safarar Miyagun Kwayoyi Jamhuriyar Nijar Ta Cafke Matasa 58