Yayi da karamar sallah ke gabatowa a Kanon Nijeriya tuni matasa masu sana'oinsu akan danjar motoci suka fara baje kolin kayayyakinsu domin cinikin sallah kowa da irin nasa sana’ar.
Matashi Yusuf Mohammad ya ce yana zuwa irin sana'oin da ya ke yi ne duba da yanayi da kuma lokaci, inda ya ke cewa a farkon watan Ramadan, ya tsunduma harkar fansar da Al Kur’ani mai girma ne ga alumma musulumi , yanzu kuwa da watan ke kan gangara ya tsunduma ga sana'ar sayar da abu awo da aka fi sani da mudun-nabiy domin auna hatsin da za;'a fitar da zakatul fitr da shi.
Matashin ya ce kafin wannan sana'a dai yana harkar sayar da faifen waka ko darussa ne a danjar manyan tituna ne, yana mai cewa shi dai yana sana’ar dai dai da lokaci da kuma abinda mutane ke bikata a lokaci.