Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Fasahar Mota Mai Tuka Kanta


Da alamu dai motoci masu tuka kansu su ne za su fi tasiri a shekaru masu zuwa, amma kada a firgita tukuna. Duk da yake cewar kamfanoni masu kera motoci sun yi gwajin wannan fasaha a kan tituna, duk da haka ba nan kusa ake tunanin samar da ita ba.

Abin da aka rasa yanzu dai bai wuce samar da karfin fasaha da zai sa mota ta sarrafa kanta tamkar yadda mutane suke yi, a lokacin da suka tsinci kansu cikin halin ‘kaka na kayi.

Basirar kirkirar mota mai tuka kanta dai ta dade ana nazarinta tun shekarar 1930, wadda ta dauki kusan shekaru 80 kafin ‘daukar abin da ake ganin ba zai yiwu ba zuwa gwaji.

Abin ya juyo ne a ranar 13 ga watan Maris na shekara ta 2004, lokacin da kamfanoni 15 suka shiga gasar neman lashe Dala Miliyan 1, da hukumar tsaro ta Pentagon ta saka.

Cikin shekara ta 2007, shekaru uku gaba, wata mota mai tuka kanta da jami’ar Carnegie Mellon ta kirkira, wadda kuma ta lashe wata gasa da akayi.

Tun wancan lokacin masu bincike a jami’ar Carnegie Mellon da sauran jami’o’i hade da sauran kamfonin kera motoci suka fara aiki tukuru don ganin sun kawo ire iren wannan motoci masu tuka kansu kan tituna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00

XS
SM
MD
LG