Gadar Gilashi Ta Farko A Duniya Tayi Karko!

Gadar Gilashi a China

A yau ake bukin cika shekara daya da kasar China, suka kaddamar da wata sabuwar gada wadda akayi ta da Gilas. Gadar na da tsawon mita dari tara da tamanin 980 Ft. Tana nesa da kasa da mittoci dari shida 600, kusan kamar ace tsawon gidan bene mai hawa ashirin 20.

An sama gadar suna “Gadar mazan jiya” wadda take cikin harabar gidan shakatawa, da ke yankin kudancin kasar China. A tabakin wani ma’aikacin kamfanin da sukayi aikin gadar, ya tabbatar da cewar gilashin da akayi amfani dashi yana da kaurin fiye da kashi ashirin da biyar 25% na sauran gilas.

Ya kuma tabbatar da amincin gilas din, da jaddada inganci da gadar keda, kana anyi amfani da karfe mai matukar mahimanci wajen karama gadar karfi. Dubun dubatan mutane sunyi tururuwa wajen tafiya akan gadar bayan suna ganin kasa. Wasu daga cikin mutane basu iya tafiya a tsaye ba don tsoron da jiri da suke gani. Kamfanin sun bayyanar da cewar yanzu haka suna kokarin samar da wata gadar irin wannan ta gilashi amma wadda motoci zasu bi, kamin nan da shekara mai zuwa.