Ado Daukaka shahararren mawakin siyasa ne da yanzu haka ya kwashe kwanaki shidda ba’a san inda yake ba, lamarin da ya kara jefa iyalansa da masoyansa cikin mawuyacin hali, hukumomin tsaro na jihar Adamawan sun tabbatar da sace wannan mawaki da aka rasa inda yake jim kadan bayan fitar da wata waka da ya raira mai taken gyara kayanka wakar dake Allah wadai da halayen wasu ‘yan siyasar jihar.
Iyalai da masoyan Ado daukaka sun bayyana wa muryar Amurka ta waya cewar rabonsu da ganin Ado tun ranar juma’ar data gabata ne yayin da ya fita daga gidansa zuwa shagonsa kamar yadda daya daga cikin matansa malama Hadiza Dauda wadda bata dade da haihuwa ba ta bayyana.
Matar tace “ranar lahadi na haihu, kuma rabuwata dashi ta karshe tun ranar alhamis daya dawo, yazo muka gaisa, ‘yar uwata ta fada mani cewa yayi sallar asuba ranar juma’a daga nan har dare bamu ganshi ba, muka cigaba da jira gasahi har yanzu bamu ganshi ba.”
Wakilin sashen Hausa na muryar Amurka ya tambayi matar mawakin cewa mai suke tunanin ya jawo wannan matsala, domin jama’a na danganta lamarin da siyasa sai ta ce ita dai tasan cewa mai gidanta baya gaba da kowa, sai dai dashiki sana’ar mawaki kila ya tabo wani a cikin wakokinsa basu sani ba. Dan haka ta mika kokon bararta ga jama’a dasu taimaka masu da addu’oi.
Hadakar kungiyar mawakan jihar sun yi Allah wadai da kuma kira ga wadanda suka sace mawakin da su taimaka domin wannan wata mai falala su sake shi domin ya koma wurin iyalansa.
Malam Hassan al’baddawi wanda ake ma lakabi da kokaga budurwa ne shugaban kungiyar jihar Adamawa kuma ya bayyana irin halin da ake ciki a yanzu cewar ko suwanene suka dauke shi, su timaka su dawo dashi domin albarkacin wannan wata.
Shugaban ya kara da cewa ‘yan siyasa su iya tunawa cewa sukan yi amfani da mawaka wajan fadakarwa a yayin da suke yakin neman zabe, dan haka bayan zabe mawaka kan duba suga idan akwai abinda gwamnati bata yi ba domin su bayyanawa jama’a.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa suna kan bincike domin tabbatar da gano wannan bawan Allah a duk inda yake.
Ga rahoton Ibrahim Abdul’aziz daga Adamawa.