Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamu Tilde: Yaro Badda Hankalin Dare Don Neman Suna A Duniya!


Adamu Tilde
Adamu Tilde

Adamu Tilde, wani matashi ne da yayi karatun allo, na tsahon shekaru bakwai 7, a gaban mahaifiyar shi, da wasu magabatan shi. Kafinnan ya shiga makarantar boko a garin Tilden Fulani, a karamar hukumar Toro, jahar Bauchi, a shekara ta 1996.

Bayan kammala karatun firamari ne a shekara ta 2000, ya tafi garin Zaria domin cigaba da karatun gaba da Firamari. Ya cigaba da zama a Zaria har shekara ta 2006, inda ya kammala karatun Sakandare a makarantar da ake kira Sheikh Ibrahim Arab Special Secondary School, Karau-Karau, Zaria.

Kammalawar shi ke da wuya, sai wuce jami’ar dake Maiduguri, inda ya kammala digirin shin na farko a fannin ilimin kiwon Dabbobi a shekara ta 2012. A tsakanin shekaru na 2013 zuwa 2014, Adamu Tilde, yayi bautan kasa NYSC a karamar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto. Bayan kammalawanshi ne a shekara ta 2014, ya rubuta jarrabawar da taba shi nasarar samun gurbin karatu na gwamnatin tarayya a kasar Hungary, domin karatun digiri na biyu.

Tsakanin shekarar 2014, zuwa watan yunin 2016, Adamu Tilde, ya kammala digiri na biyu a fannin ilimin kwayar halitta na dabbobi. Sai ya samu babbar nasarar kammala karatun shi da sakamako mafi girma “Distinction”. Dadi da kari, binciken da yayi lokacin karatunshi a Hungary, ya samu yabon bincike mafi kyau, da daraja a dukkan binciken da akayi a matsayin karatu na “Master degree” a jami’ar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG