An Fara Takun Saka Tsakanin Kamfanin Facebook Da Kasashen Turai!

Kamfanin Facebook

Kungiyar kasashen turai “Europe Union” a turance, suna wani yunkurin bazama kamfanin shafin zumunta na facebook wuta. A cewar su, shafin zumuntar na daukar bayanan sirrin mutane a yankin, yana bama gwamnatin kasar Amurka.

Wata kotu a nahiyar kasashen turai din, ta bada hukuncin cewar kamfanin ba zai bada bayanan jama’a ga gwamnatin Amurka ba. A dalilin haka, kotun ta sanar da kamfanin wata yarjejeniya, da suka sama hannu a tsakanin kasar Amurka da daukacin kasashen turai a shekarar 2000. Don mutunta juna da karrama abokantaka.

Ana zargin kamfanin da tara bayanan jama'a, a dakin tara bayanan su na kasar Amurka. Kotun na ganin cewar wannan yarjejeniyar bata aiki, sun kuma kara da cewar ya kamata kasashe masu zaman kansu, su haramta ma kamfanonin kasar Amurka, daukar bayan jama’ar kasar su. Sun kuma bukaci kasar Amurka, da ta mutunta hakkokin bil’adam da bayanan sirrin su. Kana masu binciken asirrin kasar Amurka, na shiga hurumin daba nasuba na binciken mutane.