Duk wata mace da ta gagara samun miji, to lallai akwai abun dubawa a kanta. A matsayin ta na mace ta taba kokarin samun namijin kirki amma bata samu ba? Ga wasu shawar’wari daga bakin masana. Idan har duk yadda kikayi wajen neman miji wanda yake sonki kuma yadamu da ke amma hakar bata cimma ruwa ba, to gwada wadannan abubuwan ki sha mamaki.
A watan azumi da ake ciki, ki kokarta wajen kyautata dangantakarki da Allah, ki bada kyauta ga mabukata. Haka ki yawaita fara'a da nafilfilin dare, da rokon Allah ya kawo miki miji nagari da kuma dacewa da sa'a a wannan rayuwar.
Ki rage yawan fada, da yawan surutu tsakanin ki da sauran 'yan uwa mata ko maza. Kada kuma azumi ya hanaki kwalliya da gyaran jiki, yadda ya kamata ace ko wace mace na yi. Kokarta wajen kamun kai, magana da kowane irin mutun, shiga harkar da bata shafe kiba, gulmar kawa ko aboki, yawaita bakinciki don kawarki nada saurayi, ke baki da shi.
To fara duba kanki, ki gani wai me kikeyi wanda ya sabama yadda sauran mutane ke gudanar da rayuwar su ta halin yau da kullun. Yima kanki adalci wajen bayyanar ma kanki da gaskiya koda kuwa baza kiji dadin yin hakan ba.
Duk idan mace ko na miji suka tsare wadannan shawarwarin a cikin wannan watan mai rahama, to ba abun mamaki bane idan Allah, ya kai rai da lafiya bayan sallah a dace da alkhairin Allah. Sai a kokarta wajen amfani da watan azumi don neman dacewar Allah, a kowane hali aka samu kai a rayuwa.