Hukumar Hisbah reshen karamar hukumar Dala , a jiya ta kama wasu matasa gandaye marasa azumi, a Sabon garin Kano, a Nijeriya, an dai kama wadannan gandaye ne da rana tsaka inda hukumarr tayi awon gaba dasu, yayi da mafi yawan su ke cewa sub a gandaye bane.
Hukumar ta ce har yanzu tana yunkurin ceto matasa gandaye marasa azumi daga halaka, inda ta ke cewa har yanzu akwai matasan da wa'azin da ake yi baya shiga jikinsu
Mataimakin kwamanda Hisban reshen karamar hukumar Dala , Mal Abubakar Salihu ya ce wannan ba dabi'a ce mai kyau ba inda ya ja hankali Malamai da su yawaita yin wa'azin laifin da ke tattare da matasa balagai da basa azumi.
Ya kara da cewa hukumar Hisbah, zata gabatar dasu gaban kotu domin Alkali, ya yake masu hukunci daya dace dasu a kai su gidan yari, yana mai cewa sun kama kimanin matasa 22, maza da mata musulmai .