Hadaddiyar Daular Larabawa Tace Daram Take Ciki Yakin Da Ake Yi A Yemen

wannan ya saba wa sanarwar da ta bayar da tace ba’a fahimce ta da kyau ba

A yau Juma’a ne gwamnatin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta tabbatar da cewa bata fitar da hannunta ba a yakin da ake a Yemen, wanda wannan ya saba wa sanarwar da ta bayar da tace ba’a fahimce ta da kyau ba.

Yarima mai jiran gadon sarauta na Abu Dhabi ne ya ruwaito wata sanarwa a shafin Twitter da ta fito daga ministan harkokin waje, Anwar Gargash, wadda ke cewa yaki a Yemen yazo karshe ga sojojinsu, bayan zama wani bangare na kungiyar hadin gwiwa da Saudi ke jagoranta a yakin da ake da ‘yan adawa sama da shekara.

Sai dai kuma yadda rubutun yake a rubutun larabci, na cewa yakin ya kusa zuwa karshe.

A yau Juma’a Gargash ya fadawa gidan cewa anyiwa sanarwar ne wata fahimta ta daban, wadda ba gaskiya bane.

An dai kori ‘yan tawayen Houthi daga biranen dake kudancin Yemen, inda shugaban kasa Abdu Rabu Mansour Hadi ya kafa sansani bayan dawowarsa kasar.

Kungiyar hadin gwiwar da Saudi ke jagoranta, ta hada ne da yawancin manyan kasashen Larabawa, kuma suna ta kai hari ta sama kan ‘yan tawayen tun watan Maris ‘din shekara ta 2015, wanda yake wani bangare na ‘kara tsaurara amfani da karin soji wanda Saudi da kungiyar hadaddiyar daular larabawa ke yi.