Shaidun gani da ido a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya sun ce mutane akalla 10 sun mutu sannan fiye da 15 sun samu raunuka bayan da wasu mayaka su ka kai hari kan wani babban otal jiya Laraba.
Wani Dan Majalisar Dokokin Somaliya mai suna Mohammed Isma'il Shuriye ya gaya ma Muryar Amurka cewa an kashe wasu 'yan Majalisar biyu: Abdullahi Jama Kaboweyne da Mohamud Gure a wannan harin. Ya ce Dan Majalisar na uku, Abdullah Hashi, rauni ya ji.
Daya daga cikin 'yan Majalisar da ke cikin otal din ya bayyana harin da cewa, "Ina kwance a daki na a otal din kenan, sai kawai wata babbar kara ta firgita ni. Wani marufin kofa da wani marufin taga suka fado kai na. Na ruga zuwa kofar baya ta otal din na tsira da rai na," a cewarsa.
Abdullya Haji ya gaya ma Muryar Amurka cewa ya ruga da wani abokinsa zuwa asibiti, inda ya ga motocin daukar marar lafiya na ta kawo dinbin wadanda su ka samu raunuka don jinya.
Wani dan jarida mai zaman kansa da ke aiki ma Muryar AMurka, ya ce ya ga gawarwaki 5 kwance a gaban otal din.
Barnar ta yi tsanani ne saboda tarwatsewar da wata mota shake da bam ta yi a daidai lokacin da ake Sallar Issha.
Harin da aka kai otal din Ambassador da ke Mogadishu din, ya zo ne 'yan sa'o'i bayan da jami'an Somaliya su ka ce an kashe wani babban kwamandan mayakan al-Shabab a wani farmakin da aka kai cikin dare sosai.
Ana zargin Mohammed Mohamud, wanda aka fi sani da Dulyaden da shirye harin da aka kai Jami'ar Garissa ta kasar Kenya a watan Afirilun 2015, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 148, galibi dalibai.