Hillary Clinton Ba Ta Bi Ka'ida Ba Wurin Amfani Da Adireshinta Na Email

Clinton

Rahoton sufeto janar na Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ne ya kwarmato

Wani rahoton sufeto-janar a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da aka kwarmato, ya nuna cewa Hillary Clinton ba ta bi ka'ida ba yayin da ta yi amfani da adireshinta na email wajen gudanar da harkokin gwamnati a matsayinta na Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka.

Ana sa ran fitar da rahoton a yau dinnan Alhamis, to amma tun jiya aka kwarmata abin da ya kunsa ga manema labarai.

Manyan jami'an Ma'aikatar Harkokin Waje sun ce babu wata shaidar da ta nuna cewa Clinton ta nemi izinin amfani da adireshin email dinta wajen gudanar da harkokin gwamnati, kuma idan da ta tambaya, da an hana ta.

Wajibi ne jami'an gwamnati su yi amfani da adireshin email na gwamnati wajen gudanar da harkokin gwamnati saboda tabbatar da tsaro da kuma kare bayanan gwamnati.

Rahoton ya yi nazarin yadda Sakataren Harkokin Wajen Amurka na yanzu John Kerry ke tafi da batun sakonnin email, da ma sauran wadanda su ka gabaci Clinton, ciki har da Condoleezza Rice, da Colin Powell da Madeleine Albright. Rahoton ya lura cewa an dade ana samun irin wadannan matsalolin, to amma ya fi mai da hankali kan yadda Clinton ta yi amfani da adireshin email dinta.