Ministocin kudin kasashen dake amfani da takardar kudin Euro sun ce sun cimma gagarumar nasara wajen cimma yarjejeniyyar ragewa kasar Girka basussukan da ake bin ta, bayan sa’o’in da suka kwashe suna tattaunawa a birnin Brussels, a daren jiya Talata.
Asusun bada lamuni na duniya da na IMF, ya bukaci a ragewa Girka bashin da ke kanta a wani mataki da Asusun na bada lamuni ya kara dauka na taimaka mata da kudade don tada komadar tattalinta na arziki.
Girka za ta karbi kashin farko na kudi dala milyan dubu 11 da miliyan 4 a cikin wata mai zuwa, biyo bayan amincewar da tarayyar Turai ta yi da kokarin yin garambawul ta fuskar tattalin arziki da kasar ta Girka ta yi kwanan nan.
Wannan shine taimako na baya-bayan nan cikin shekaru 6 da Girka ta samu, kasar da ta yi ta fama da matsalolin tattalin arziki wanda ya jefa ta cin bashin da yawansa ya ribanya kuddin shiga da dake samu sau 180.