Ya Fi Kama Da Aikin Ta'addanci Fiye Da Matsalar Na'ura.

Ya Kamata mu tabbatar mun san duk wani abin da ke da nasaba da abin da ya faru

Ministan Sufurin Jirgin Saman Masar ya ce masabbabin faduwar jirgin saman Masar wanda ke kan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira daga birnin Paris, ya fi kama da aikin ta'addanci fiye da duk wata matsalar na'ura.

Ministan Sufuri Sherif Fathy ya yi magana kan faduwar jirgin ne a yayin da ake cigaba da nemar tarkacen jirgin mai dauke da mutane 66 a yankin Tekun Meditareniya, wanda ya bace daga mahangar rada a yau dinnan Alhamis, jim kadan da shigarsa sararin saman Masar a tafiyarsa mai tsawon sa'o'i 4 daga Faransa.

Rahotannin farko daga kasar Girka na nuna cewa an hango wasu abubuwan da ake kyautata zaton tarkacen jirgin ne. Amurka na taimakawa wajen aikin ceto da kuma gano jirgin daga sararin sama, ta wajen amfani da jirgin nan samfurin P-3 Orion mai dogon zango.

Ya kamata mu tabbatar mun san duk wani abin da ke da nasaba da abin da ya faru. Ba a mai da hankali kan wani hasashe guda kawai ko kuma kawar da shi ba," a cewar Shugaba Francois Hollande ga manema labarai a birnin Paris, a yayin da ya ke tabbatar da faduwar jirgin. Ya ce gwamnatin Faransa na aiki tare da hukumomin Masar da Girka wajen nemar baraguzan jirgin.

Kamfanin jirgin na EgyptAir ya ce tuntuba ta katse tsakaninsa da jirgin samfurin Airbus A320 da misalin karfe 2:30 agogon Alkahira, yayin da jirgin ke da nisan mita 11,000 daga kasa kuma ya shiga sararain saman Masar da nisan kilomita 16 kawai.