Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Daya Daga Cikin 'Yan Mata Chibok Da Danta


An dai gano wannan yarinyar ne a wani kauye dake tsakanin wani gari da ake kira Bali da dajin Sambisa

Wasu bayanai dake fitowa da dumi dumi na nuni da cewa an gano daya daga cikin ‘yan makarantar mata na Chibok,da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace tun shekaru biyu da suka gabata.

An dai gano wannan yarinyar ne a wani kauye dake tsakanin wani gari da ake kira Bali da dajin Sambisa, inda ‘yan Kato da Gora da rundunar Sojoji suka shiga domin gudanar da sintiri.

Tuni dai aka mika wanna yarinya ga jami’an tsaro dake karamar hukumar Dambuwa, domin ci gaba da gudanar da bincike a kanta.

Malam Afagu, na daya daga cikin jami’an sintirin da suka gano wanna yarinya kuma ya kasance da garin Chibok, ya tabbatarwa wakilin muryar Amurka Haruna Dauda, cewa ya ga yarinyar da idon sa har ma kuma sun kai yarinya ga iyayenta kafi amika ta ga jami’an tsaro.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG