Kwamandan rundunar sojojin Amurka mai kula da Afirka, da ake kira AFRICOM a takaice, ya fada cewa, dakarun Amurka na shirye su taimakawa tawagar da za ta horas ta kuma samar da kayan aiki don yakar dubban mayakan ISIS a Libya duk lokacin da gwamnatin Libya ta shirya.
Kwamanda rundunar ta AFRICOM, General David Rodriguez ya kara da cewa siyasar Libya ta sa ba za a iya gane wadanne mayaka ne ke bangaren gwamnatin hadin kan kasa da ake kira GNA a takaice, abinda ya sa Amurka dogaro ga gwamnatin wucin gadin kasar don tantance wake tare da ita ko wake adawa da ita.
Yace ta yiwu dakarun su ne zasu hana bazuwar mayakan ISIS da zarar an gane mayakan da ke goyon bayan gwamnati an kuma taimaka masu.
Yanzu haka dai kasar Libya na karkashin dokar ta-bacin da aka kafa na hana saida mata makamai don a tabattarda makaman basu kai hannun 'yan ta'adda ko mutanen dake kokarin gyara zamansu akan kiujerar mulkin kasar ba.