Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe A Kalla Mutane 28 A Wani Harin Boma A Kasar Iraq


A cikin makon guda da ya shige, kungiyar ISIS ta dauki alhakin hara hare a ciki da kewayen Bagadaza da ya kasha mutane 100

An kashe a kalla mutane 28 wadansu sittin da shida kuma suka yi taunuka a wani harin boma bomai da aka kai yau talata a babban binrnin kasar Iraq.

Kazamin harin da ya yanjo asarar rayuka ya auku ne a yankin kungiyar al-Shaab dake arewacin Bagadaza inda jami’ai suka ce wata mace ‘yar kunar bakin wake ta tarwatsa nakiyoyi a cikin kasuwa.

A wani harin na dabam, wata mota da aka dankare da makamai ta tarwatse a unguwar rashid dake kudancin birnin.

Nan da nan babu kungiyar da ta dauki alhakin harin.

A cikin makon guda da ya shige, kungiyar ISIS ta dauki alhakin hara hare a ciki da kewayen Bagadaza da ya kasha mutane 100.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG