Hakan ma na alakanta biyawa kwadagon bukata don kawar da batun yajin aiki daga karewar wa’adin na gobe Laraba, na neman dawo da litar Mai Naira 86. Ba alamar gwamnati zata ja da baya haka nan itama kungiyar Kwadagon dake samun gwalewa daga sassan ma’aikata da talakawa dake cewa ba zasu marawa yajin aikin baya ba.
A baya dai ministan Kwadago Chris Ngige, ya jaddada gwamnati zata samar da karin ayyukanyi maimakon rade radin rage ma’aikata. Haka kuma yayi karin haske kan tanadin da kasafin kudi yayiwa ma’aikata.
Shi kuma shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya, Ibrahim Khalil, ya nuna ba lalle bane karin albshin ne damuwar ba, amma yadda farashin kayayyaki ke tashin gwauron zabi.
Alamu na nuna matakin kungiyar Kwadagon kan iya samun tasiri ko matsakaicin tasiri a wasu yankuna da jam’iyyun adawa ke da tagomashi da kuma tsakanin talakawan dake ganin ba ranar karewar talauci a Najeriya.
Domin karin bayani.