Maradun Gwamnati A Takarda Tabas Maradu Ne Masu Kyau

Amma tun daga hawar wannan gwamnati kawo yanzu hakuri ake baiwa mutane

Masana da yan Najeriya na ci gaba da tsokaci bisa yadda gwamnatin tarayya tace zata samar da guraben ayyuka da kudadaden tallafin mai da aka cire.

Wani dan jarida kuma mai sharhi kan alamuran yau da kullum, Hassan Gimba Ahmed, yace gwamnatoci sun sha fadin abubuwan da zasu yiwa jama’a, amma ba’a gani a kasa, ita gwamnati tana da abu biyu dake tattare da ita.

Na farko ba’a taba yin gwamnati da ita kamar wannan ba domin ana ganin cewa shugabanta Muhammadu Buhari, mai kwatanta gaskiya ne da kuma rikon amana, na biyu kuma ba’a taba gwamnati da aka juma jama’ar kasa na mata uzuri ba kamar wannan ba, wannan kuma ya biyo bayan ganin cewa gwamnatin nada nufin alheri ga al’umar kasa ne.

Yana mai cewa yana ganin cewa idan aka yi hakuri aka kara baiwa gwamnatin lokaci zuwa karshen shekaran nan za’a ga ko za’a ci gaba da yarda da ita kuma cewa yadda aka dauketa mai amana aka ganta mai gaskiya shin zata cika wannan ko bazata cika ba.

Shi kuwa Malam Imam Gashua, cewa yayi maradun gwamnati a takarda tabas maradu ne masu kyau amma yana kokwanto wajen aiwatar dasu domin tun daga hawar wannan gwamnati kawo yanzu hakuri ake baiwa mutane tun jama’a, na uzuri yanzu sun fara kokawa, ya kara da cewa baya tunanin cewa abinda aka ce za’a yi zai aiwatu sai dai ya gani a kasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Maradun Gwamnati A Takarda Tabas Maradu Ne Masu Kyau - 2'14"