An Kammala Taro Akan Ta'addanci Da Limamai

Dalilin wannnan taron shine ganin yadda duniya ke fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda wadanda ke fakewa da addini

Kungiyan limaman Musulunci na kasar Kamaru sun kammala wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu a birnin Yaoundé babbar birnin kasar Kamaru.

Dalilin wannnan taron shine ganin yadda duniya ke fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda wadanda ke fakewa da addini wanda kuma kasar ta Kamaru ta tsinci kanta a cikin wannan halin masamman ta arewacin kasar inda kasar tayi iyaka da Najeriya, inda ‘yan ta’addan Boko Haram ke kai ruwa rana da dakarun kasar Kamaru.

Kanin haka yasa aka shirya wannan taro na karawa juna sani da irin matakan da Limamai zasu dauka wajen wayarwa da jama’a kai domin gujewa duk wani nau’i na ta’addanci, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Shugaban Limaman kasar Kamaru, Dr. Musa Umaru, ya yabawa dukkan Limaman kasar na amsa kiran da suka yi da fatan kowa zai taimaka wajen samun zaman lafiya.

Limamin jihar yamma na kasar Kamaru,Sheikh Haruna Abdullahi, da na jihar arewar yamma Sheikh Tukur sun ce zamatakewa tsakanin Musulmi da Kirista yana tafiya kamar yadda ya kamata.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kammala Taro Akan Ta'addanci Da Limamai - 2'51"