Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Garin Fort McMurray dake Canada da gobara ta addaba ya tsira


Jirgin kashe gobara
Jirgin kashe gobara

Firimiyar Alberta ta kasar Canada Rachel Notley tace, kusan kashi 90 na birnin Fort McMurray ya tsira daga masifar wutar dajin da ta dinga ci ba tare da an iya shawo kanta ba.

A baya Notley da hukumomin garin sun yi ammanar cewa, wutar ta cinye ilahirin birnin, to sai gas hi a shawagin da aka yi ta sama a jiya Litinin ya nuna cewa wurare kadan ne wutar ta cinye ba yadda aka yi zato ba.

Ta bayyana cewa, “wuta da ta tashi gadan-gadan a garin a kwanakin da suka shude, sai gashi birnin Fort McMurray da alummarsa sun tsira, sannan za’a taimakawa mutanen garin”. Inji Notley.

Ta kuma godewa ma’aikatan kashe gobara game da kokarinsu da suka yi don cetar garin daga babbakewa, duk kuwa da rasa wutar lantarki da ruwan fanfo. Firimiyar tace zai kai mako daya nan gaba kafin al’ummar birnin su koma muhallansu.

Jami’ai a kasar suka ce, wutar dajin tana ta ci har a jiya Litinin, amma cikin ikon Allah sai aka sami canjin yanayin sanyi da kuma ruwan sama, wanda ya taimaka matuka wajen baiwa masu aikin kashe gobarar kwarin gwiwa.

Alberta dai nan ne gari na uku a duniya da suka fi ko ina ajiye rarar man fetur in ka dauke kasashen Saudiyya da Venezuela. Sannan wutar bata kai kan ko daya daga cikin harabar da gangunan man fetur din suke ba.

Gobarar Fort McMurray
Gobarar Fort McMurray

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG